Kamar yadda wata majiyar tsaro soja a kasar ta shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP ta ce wasu daga cikin sojojin sun mutu ne yayin da wasu motici biyu shekeda boma-bamai suka aukawa ayarin motocin na su, yayinda sauran suka mutu a musayar wuta da mayakn islaman dake rikeda iko birnin Benghazi. A ranar 16 ga watan Mayu ne Genar Haftar na sojan Libiya ya kaddamarda yaki kan mayakan islama na Ansar Asharia a Libya kungiyar da hukumomin kasar da Amurka suka ayana a matsayin kungiyar ta’adanci dake aiwatarda hare-hare da kitsan jama’a a birnin Benghazi, inda wasu alkalumen hukimomin lafiya suka nuna cewa mutane 79 ne aka yi wa kitsa a watan Sebtemba daya wuce kwai. ABNA
3 Oktoba 2014 - 08:31
Lambar labari: 641976
Akalla sojoji 13 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 70 na daban suka raunana a wani kazamin fada da akayi tsakanuin dakarun sojan kasar Libya da kuma mayakan islama a gewayen filin sauka da tsahin jiragai sama na birnin Benghazi dake gabashin kasar.